Za a Fuskanci Matsalar Ambaliyar Ruwa a Daminar 2023 – NEMA

 

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce za a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a daminar 2023.

Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, lokacin wani taro da hukumar ta shirya.

Duk da hukumar ba ta fayyace wuraren da ambaliyar za ta fi shafa ba, amma ta ce shiryawa da wuri zai taimaka wurin rage ɓarnar da ambaliyar za ta iya haifarwa.

A daminar da ta gabata an samu mummunar ambaliya a yankunan Najeriya daban-daban, wani abu da ya yi sanadin rayuka da dukiya mai ɗinbin yawa.

A kan haka ne hukumar ta shirya taron ƙara wa juna sani ga ma’aikatanta da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kare faruwar bala’o’i.

Mustapha Ahmed ya ce “babu ko shakka za a samu ambaliyar ruwa a wannann shekarar, ba mu san irin ɓarnar da za ta yi ba amma tabbas za a samu ambaliyar ruwa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here