Duba Kayan Zaɓe: Tawagar Lauyoyin Jam’iyyar LP na Ganawa da Hukumar INEC

Tawagar lauyoyin jam’iyyar LP na ganawa da jami’an hukumar zaɓen Najeriya a Abuja babban birnin ƙasar.

An ganawar ne a shalkwatar hukumar zaben ƙasar domin fara duba kayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ana sa ranar tawagar lauyoyin 60 ƙarƙashin jagorancin Dakta Livy Uzoukwu, za su yi manema labarai bayanai bayan ganawar.

Jam’iyyar ta LP dai ta shigar da ƙara gaban kotu, inda ta nemi kotun ta ba ta damar duba kayayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su, bayan da jam’iyyar ta yi zargin tafka maguɗi a zaɓen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here