Hasashe Ya Nuna Cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na Hararar Muhimman Kujeru 2 a Zaɓen 2023
Yanzu kallo ya koma sama yayin da yan siyasa ke shirye-shirye don samun tudun dafawa a babban zaben kasar na 2023 da ke kara gabatowa.
Hasashe sun nuna cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano yana hararar daya daga cikin muhimman kujeru biyu a babban zabe mai zuwa.
Wadannan kujeru sune na mataimakin shugaban kasa ko kuma na dan majalisar dattawa.
Kano – Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano yana auna tsare -tsaren ficewarsa da makomar siyasarsa bayan sauka a kujerar gwamna.
Ganduje ya fito fili ya ce ba shi da niyyar barin siyasa bayan ficewarsa daga gidan gwamnati, jaridar The Nation ta rawaito.
Dan siyasar mai shekaru 71 ya ce zai ci gaba da yin siyasa bayan karewar wa’adin mulkinsa na biyu a 2023. Sai dai kuma, bai bayyana kai tsaye ko zai sake tsayawa takara ba ko a’a.
Ganduje, wanda ya shiga harkar siyasa tun 1978, ya ce idanunsa za su kasance a bude don amfanin kasa.
A lokacin da jaridar The Nation ta tambaye shi ko zai bi tafarkin takwaransa na jahar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda y ace zai bar siyasa a 2023 sai ya ce:
“Ban gaji ba ta koina; ba kuma zan yi murabus ko ritaya daga siyasa ba.”
Read Also:
Gwamnan yana lura da guguwar siyasa yayin da iskar ke kadawa. Makusantansa sun ce yana neman muhimman mukamai guda biyu yayin da yake duba hukuncin da jam’iyyarsa ta APC zata yanke.
Baya ga gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen gina jam’iyya mai mulki, Ganduje yana da kusanci da manyan jiga -jigan jam’iyyar APC da suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Haka kuma a lokuta daban -daban ya karbi bakuncin Muhammadu Buhari da jagoran jam’iyyar, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, inda aka rawaito sun tattauna makomar jam’iyyar mai mulki.
Duk da haka, damar sa ta zama ɗan takarar shugaban ƙasa ya dogara da shawarar jam’iyyar.
Ba za a iya rinjayar tasirin Ganduje a babban zaben 2023 ba, idan aka yi la’akari da dimbin masu jefa ƙuri’a a Kano, wanda shine dalilin da ya ba Buhari nasara akan Goodluck Jonathan a 2015.
“Idan burinsa na zama mataimakin shugaban kasa bai yi nasara ba, Ganduje zai koma ga Majalisar Dattawa,” in ji wani na kusa da shi.
Idan ya tsaya takarar Majalisar Dattawa, zai fuskanci wasu matsaloli ne kawai da zai tsallake.
Ya ce:
“Shugabancin jam’iyyar APC ya riga ya shirya mika masa tikitin takarar, idan yana da burin zama sanata, bayan haka, Sanata Barau Jibrin sanata mai ci wanda ke wakiltar gundumar Kano ta Arewa inda gwamnan ya fito, yana takarar gwamna.”