EndSARS: Gwamna Ganduje ya Bai Yana Wanda Suka Lalata Zanga -Zangar

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi ikirarin cewa wasu mutane wanda basa son ganin ci gaban Najeriya ne suka bata zanga zangar #EndSars

Ganduje ya bayyana cewa ainihin zanga zangar da aka fara don nuna rashin amincewa da zaluncin ƴan sanda tana da dalili mai karfi

Gwamnan ya ce maƙiyan Najeriya ne suka haddasa fitina a cikin zanga zangar saboda bukatar su Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan Kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin manyan jami’ai suna goyon bayan zanga zangar lumana ta #Endsars da aka fara don nuna kyamatar zaluncin ƴan sanda. Sai dai, Gwamnan ya yi iƙirarin cewa maƙiyan Najeriya ne suka yi amfani da yanayin wajen ganin sun rusa kasar.

A cewar Ganduje

“Asalin zanga zangar ana magana ne akan zaluncin jami’an SARS da kashe mutane ba bisa ka’ida ba, wanda babbar matsala ce kuma da yawan mu mun goyi bayan zanga zangar, tare da yin kira da ayi wa hukumar ƴan sanda kwaskwarima

nAmma abun da ke faruwa yanzu ya tabbatar da cewa; maƙiyan Najeriya ne suka zauna suka kuma yi shawarar bari su rusa ƙasar. Amma Allah yana tare damu; basu yi nasara ba.” Ya kuma bayyana cewa duka mai addu’ar ganin bayan Najeriya cikakken mahaukaci ne, ya kuma yi kira da hadin kan ƙasa, musamman daga matasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here