An Gano Cewa Miyagu na Shirin Kai Hare-Haren Bam da Karamar Sallah – ‘Yan Sandan Najeriya

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar da wata sanarwa cewa akwai yiwuwar wasu miyagu su kai hare-haren bam kan al’umma yayin karamar sallah mai zuwa wadda ta kawo karshen watan Azumin Ramadan.

Cikin sanarwar, kakakin Rundunar Peter Afunanya ya ce an gano wani shirin da wasu kungiyoyi suka kitsa domin kai hare-haren kan wasu mhimman wurare da masallatai da kuma wuraren shakatawa.

Wannan gargadin na zuwa ne bayan da wasu abubuwa suka fashe a mashaya a jihohin arewa maso gabashin Najeriya biyu – Yobe da taraba – inda mutane da dama suka halaka.

Wani tsagin kungiyar Boko Haram da aka fi sani da ISWAP ne ta dauki alhakin kai hare-haren.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here