An yi Garkuwa da ɗalibar Jami’ar Bayero ta Kano

Rundunar ‘yan sanda a jahar Kano arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da sace wata budurwa mai shekara 23, daliba a Jami’ar Bayero ta Kano da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka dauke ta.

A cewar kakakin ‘yan sandan jahar ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun sami labarin sace budurwar ne sakamakon kira da suka samu na ɓatan ta daga wani mutum tun bayan fitar ta ziyara unguwar Kuntau, kuma ba a sake ganin ta ba.

Jahar Kano dai na daga cikin jahohi dake makawabtaka da Kaduna, da Katsina da ake fama da matsalar masu satar mutane dan neman kudin fansa.

Sai dai Rundunar yan sanda Kano ta ce duk da samun ayyukan masu garkuwa da mutane da aka yi a jahar, suna daukar matakai kan wannan lamari, ta hanyar samar da rundanar tsaro ta hadaka masu sintiri a fadin jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here