Dan Majalisa: Masu Garkuwar Sun Nemi Kudin Fansa
Masu garkuwa da mutanen da suka sace Honourable Bashir Muhammed sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi.
Honourable Muhammed ya kasance mamba a majalisar dokokin jihar Taraba.
Wasu yan bindiga ne suka sace dan majalisar a gidansa da ke Jalingo, babbar birnin jihar Taraba a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba.
Read Also:
Wani rahoto daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa wadanda suka sace Bashir Muhammed, dan majalisa a majalisar dokokin jihar Taraba, sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi.
An sace Muhammed, wanda ke wakiltan mazabar Nguroje a karamar hukumar Sardauna da ke jihar, a gidansa da ke Jalingo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba.
A cewar rahoton, Muhammed ya roki shugabannin majalisar dokokin Taraba da gwamnatin jihar a kan su biya bukatar wadanda suka sace shi domin ceto rayuwarsa.
A cewar wata majiya a rahoton, mambobin majalisar sun hadu da Gwamna Darius Ishaku kan lamarin.