Masu Garkuwa da Mutane Sunyi Garkuwa da Mahaifiyar ‘Dan Majalisar Dokokin Jahar Neja
‘Yan bindiga sun kai hari jahar Neja a daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da mahaifiyar wani dan majalisa, Honarabul Bello.
Rahoton ya nuna cewa tuni masu garkuwan suka tuntubi dan majalisar inda suke neman kudin fansa na N100m.
Satar matar mai shekaru 78 na zuwa ne a ranar da aka kashe mutane biyu sannan aka sace wasu daga karamar hukumar Rafi.
Wasu rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Hajiya Salamatu Ahmadu, mahaifiyar dan majalisar dokokin jahar Neja, Alhaji Bello Ahmed Agwara mai shekaru 78.
Jaridar ThisDay ta rahoto cewa an sace tsohuwar ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Alhamis, 29 ga Afrilu.
Read Also:
A cewar rahoton, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai wadanda suka zo kan babura hudu sun afkawa gidan dan majalisar dokokin jahar Neja da ke garin Agwara.
Ganau sun bayyana cewa masu laifin sun fara yin harbi ba kakkautawa yayin da mutane suka tsere don tsiratar da ransu.
An tattaro cewa yan bindigan sun nufi gidan dan majalisar inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma wasu mazauna garin zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama a Tegina da ke karamar hukumar Rafi ita ma a wannan ranar.
Lokacin da jaridar ThisDay ta tuntube shi, wani babban jami’in majalisar dokokin jahar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da sace mahaifiyar dan majalisar.
Jami’in ya ce:
“Mun je gidansa a Minna don yi masa jaje.”
Rahoton ya nuna cewa tuni yan fashin suka yi magana da dan majalisar kuma suna neman a biya su N100m kafin matar ta samu yancinta.
Duk kokarin da aka yi don tuntubar Agwara ya ci tura saboda bai daga kiran wayarsa ko amsa sakonnin tes.