Masu Garkuwa da Mutane Sun Sace Mata Mai Shekaru 45 da Yaranta 2 a Abuja
Masu garkuwa da mutane sun sace wata Oladapo Bukola, mai shekaru 45 da yaranta mata guda biyu a wuraren Kuje dake Abuja.
An sace su ne bayan kwana biyu da aka sace wani Abdullahi Benda da dan sa Jibrin a wani kauye na Yangoji da ke wuraren Kwali a Abuja.
Lamarin ya faru ne wuraren karfe 1:04 am na ranar Lahadi kamar yadda wani makwabcin su, Abednego ya tabbatar.
Abuja – Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata mai suna Mrs Oladapo Bukola mai shekaru 45 da yaran ta 2 a wuraren Pegi da ke Kuje a Abuja.
Daily Trust ta rawaito cewa, hakan ta faru bayan kwana 2 da sace wani Abdullahi Benda da yaronsa, Jibrin Abdullahi Benda mai shekaru 23 a kauyen Yangoji da ke Kwali a Abuja.
A cikin yaran matar akwai Moyo Oladapo, mai shekaru 17 da wata Glory Oladapo mai shekaru 14.
Mazaunin yankin, Abednego ya ce lamarin ya faru ne da misalin 1:04am na ranar Lahadi.
Read Also:
A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun zo da bindiga kirar AK-47, inda suka kai farmaki har gidan ta da ke Zone A.
A cewar sa, sun tsallake katangar gidan matar ne sannan suka balla kofar, Daily Trust ta wallafa.
Shugaban kungiyar cigaban Pegi (PECDA), Mr Taiwo Aderibigbe ya tabbatar da satar matar da yaran ta yayin tattaunawa da manema labarai.
Shugaban PECDA ya koka a kan yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin kuma ya bukaci taimakon jami’an tsaro.
“Lamarin ya na da ban tsoro, yanzu Pegi da Kuje sun zama wurin da masu garkuwa da mutane suke kai farmaki kuma jami’an tsaro ba sa wani kokari,” a cewar sa.
Daily Trust ta rawaito yadda mijin matar, Fasto Gabriel Oladapo, ya yi tafiya lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kai farmakin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’ar ‘yan sandan Abuja, ASP Daniel Y Ndiparya, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace suna iyakar kokarin ganin sun ceto su.
“Yan sanda su na ta kokarin ganin an ceto su,” a cewar sa