Anyi Garkuwa da Wani Shugaban APC

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun shiga har gida tare da yin awon gaba da shugaban jam’iyyar APC a jihar Nasarawa.

Kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe ya sanar, lamarin ya faru wurin karfe 11 na daren Asabar.

Ya ce tuni jami’an tsaro suka gaggauta bazuwa a cikin dajin jihar domin tabbatar da sun ceto shugaban jam’iyyar Shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce ‘yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.

Gidan na kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a Lafia. Sun isa gidan wurin karfe 11 na dare inda suka yi awon gaba da shi.

Longe ya tabbatar da cewa hukumar tsaro sun gaggauta daukar mataki ta hanyar tura jami’ansu wurare mabanbanta a dajin jihar domin tabbatar da an ceto shugaban jam’iyyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here