Yadda Aka Gano Gawar ‘Dan Sanda, Matarsa da Yaransa 5 a Jahar Osun

 

Wani jami’in dan sandan Nigeria da matarsa da yara biyar sun rasu a gidansu a Osun.

Mutanen unguwa sun gano hakan ne bayan sun balle kofar gidan da safiyar Talata.

Rundunar yan sandan jahar Osun ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma fara bincike.

Isokan, Jahar Osun – Wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Elegbaata, Oke Suna, Apomu, karamar hukumar Isokan a jahar Osun bayan an tsinci gawar mutum bakwai – miji, mata da yaransu biyar – a cikin gidansu, The Punch ta ruwaito.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an ceto mutum daya daga iyalansu wanda shima ya kwana a gidan an garzaya da shi asibiti a Apomu, inda ake ba shi kulawa.

Wani mazaunin garin, da ya nemi a sakayya sunansa, ya ce mutum takwas ne suka kwana a gidan a ranar Litinin, amma an tsinci gawar bakwai da safen ranar Talata.

Yadda mutanen gari suka gano abin da ya faru?

Mazaunin ya ce mutanen unguwar sun damu ne bayan an lura cewa gari ya waye amma kofar gidan na rufe.

Majiyar ta kara da cewa: “Duk da hakan, ba mu san cewa wadanda suka kwana a gidan sun mutu ba sai lokacin da wasu suka yi karfin hali suka balle kofar gidan.

“Abin da muka gani ya razana mu. dukkansu da suka kwana a gidan sun mutu illa mutum daya; miji, mata, yaransu biyar duk sun mutu. Amma an ceto mutum daya da ransa an kai shi asibiti.

Wasu mutanen da suke nan lokacin da aka bude gidan sun ce sun shaki warin wani kemikal, amma ba zan iya tabbatarwa shine ya kashe su ba.

“Matar ce ke da gidan da abin ya faru. Mutumin da ya mutu a gidan mijinta ne, amma yaran ba nashi bane. Mutumin yana da gidansa a Apomu. Dan sanda ne mai suna Saheed.”

Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin Kakakin yan sandan jahar Osun, Yemisi Opalola ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce:

“An dauke gawar wadanda suka rasu an kai asibiti don gwaji. An kai su asibitin koyarwa na OAU, Ile-Ife. An fara bincike, duk da cewa ba a kama kowa ba.

“Mutumin da ake ceto yana samun kulawa a asibiti mai zaman kansa a Apomu; yana samun sauki.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here