Neman Takarar Gwamnan Legas a 2023: Femi Gbajabiamila ya Musanta Jita-Jitar

 

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya musanta rahoton cewa yana shirin tsayawa takarar gwamna a 2023.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa gwamnan jahar Lagos na yanzun yana yin abinda ya dace ga al’umma.

Ya kuma kara da cewa a halin yanzun ya maida hankali ne kan mukaminsa na shugaban majalisar wakilai.

Abuja – Kakakin majalisar dokokin Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai nemi takarar gwamnan jahar Lagos a 2023, kamar yadda the nation ta rawaito.

Kakakin majalisar yace tunanin neman kujera mai lamba ɗaya a jahar Lagos bai taɓa zuwa cikin zuciyarsa ba.

Gbajabiamila ya kara da cewa gwamnan Lagos mai ci, Babajide Sanwo-Olu, yana yin abinda ya dace ga al’ummar jahar duk da halin da ake ciki.

Kakakin majalisar ya bayyana haka ne a wata fira da kafar watsa labarai ta Channels tv.

Yace fara tunanin neman wani mukami a babban zaɓen dake tafe tun yanzun zai iya hana shi gudanar da aikinsa yanda ya kamata.

Ina son maida hankali kan aikina – Gbajabiamila

A jawabinsa, kakakin majalisar yace:

“Ina da ayyuka a gabana yanzun, bana bukatar duk wani abu da zai ja hankali na. Na sanar da makusanta na cewa ina son maida hankali ne kan mukamina da aikina na yanzu.”

“Bani da wani shirin zama gwamna, kuma gwamnan mu na yanzun yana aikin da ya kamata. Maganar cewa ba’a maimaita gwamna a baya, ba shi ke tabbatar da hakan zata cigaba da kasancewa ba.”

“Gwamnan jahar Lagos na yanzun yana kokarin yin abinda ya dace duk kuwa da halin matsin da ake ciki.”

Inason kafa tarihi a kujerar kakaki

Kakakin majalisar yace yana son nan gaba a rinka tuna cewa, wani ɗan majalisar wakilai da ya shugabanci majalisa, ya yi aiki tukuru wajen cigaban ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here