Gobara ta Lalata Shaguna da Dama a Kasuwar Singa da ke Jihar Kano

 

Yan kasuwa a kasuwar Singa ta jihar Kano sun gamu da babban ibtila’i a ranar Litinin, 13 ga watan Maris.

Mummunar gobara ta lakume dukiya a kasuwar da ta yi suna wajen siyar da kayan abinci.

Hukumar kashe gobara na ta kokarin daidaita wutar wacce ta fara ci tun da tsakar daren ranar Lahadi.

Labari da muke samu daga Freedom Radio shine cewa har yanzu ba kai ga kashe gobarar kasuwar Singa ta jihar Kano.

Mummunar gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta siyar da kayan abinci ta Singa da ke jihar Kano a tsakar daren Lahadi wayewar garin Litinin, 13 ga watan MariS.

Wasu da abun ya faru a kan idanunsu sun bayyana cewa gobarar ta fara ci ne a tsakar dare kuma an gagara shawo kanta har zuwa wayewar garin Litinin, rahoton Aminiya.

Jami’an hukumar kwana-kwana da ke kashe gobara suna nan suna ta kokarin shawo kan wutar wacce ke ci gaba da ci a bangarorin kasuwar.

Yanzu haka da yawa a cikin yan kasuwar na ta kokarin kwashe iya abun da ya sawwaka daga dukiyoyinsu da suka yi saura a kasuwar ta Singa.

A halin da ake ciki, an tattaro cewa gobarar ta lakume shaguna da rumbunan ajiya da dama, wanda hakan ya sa yan kasuwar asarar miliyoyin Naira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here