Gobara ta Lalata Shaguna 150 a Kasuwar Ƴan Katako da ke Zariya

Akalla shaguna 150 ne gobara ta lalata a kasuwar ƴan Katako da ke Zariya a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na dare lokacin da mutane ke barci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban masu samar da tsaro na kasuwar, Hamisu Buhari na cewa gobarar ta tashi ne lokacin da hukumar samar da wutan lantarki da KEDCO ta dawo da wuta, inda wani igiyar wutar lantarki ta faɗa kan ɗaya daga cikin shagunan.

Ya ce daga nan ne kuma wutar ta yaɗu zuwa sauran shaguna da ke cikin kasuwar, inda ya ce duk wani kokari na kiran jami’an kashe gobara ya ci tura.

Ya ƙara da cewa gobarar ta ƙona shaguna sama da 150 kurmus da kuma asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Da aka tuntuɓi shugaban hukumar ta KEDCO, Abdul Azeez Abdullahi, ya musanta cewa wutar lantarki ce ta jawo tashin gobarar.

A baya-bayan nan dai ana samun tashin gobara a yawancin kasuwa da ke faɗin Najeriya, inda ake asarar dukiya ta miliyoyn naira.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here