Kungiyar Addinin Kirista ta Nuna Goyan Bayanta Kan Matakin da Shugaba Buhari ya Dauka na Rashin Biyewa Masu Nema a Sauke Pantami

 

Wata kungiyar malaman addinin kirista ta yi tattakin nuna goyon baya ga ministan sadarwa da tattalin arziki na zaman, Dr Isa Ali Pantami.

Bishop Abel King, jagoran masu tattakin ya ce suna goyon bayan matakin da Buhari ya dauka na rashin biyewa masu neman a sauke Pantami.

Malaman addinin kiristan sun ce wasu makiya Nigeria da son zaman lafiya ne ke neman a sauke Pantami saboda aikin da ya ke yi Kungiyar.

malaman addinin kirista na ‘Forum of Christian Bishops and Clergy Council’ ta nuna goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan matsayarta game da zargin da ake yi wa ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr Isa Ali-Pantami.

Kungiyar ta sanar da hakan ne yayin wani tattaki na goyon baya da ta yi a Unity Fountain Abuja, inda ta ce wadanda ke zargin wasu tsirarai ne a kasar da basu son sauye-sauyen da ministan ke yi.

Malaman addinin na kirista sun fito rike da takardu masu rubutu da ke nuna goyon baya da ga gwamnatin Buhari da rokonsa ya cigaba da hada kan yan kasa.

Har wa yau, kungiyar ta ce ta yi tattakin ne na zaman lafiya domin jadada bukatar zaman lafiya da hadin kai a kasa.

Bishop Abel King, jagoran masu tattakin ya ce ya zama dole su fito su bayyana matsayarsu saboda irin zargin da ake yi wa Mr Pantami.

“Shugaban kasa bisa hikimarsa ya nuna cewa Nigeria ne ke gabansa kuma zai cigaba da hada kanmu sannan ba zai bari masu son kai su rude shi ba ko tilasta shi,” wannan abin yabo ne in ji Bishop Abel.

Bishop Abel ya cigaba da cewa ya kamata mutane su dena la’akari da banbancin addini, kabila ko yanki idan za su dauki mataki sai dai su mayar da hankali kan abin da zai kawo cigaba a kasa. Kazalika, ya gargadi mutane kan furta kalaman da ka iya tada zaune tsaye a kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here