2023: Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Nasarawa ya Bayyana Wanda Suke Goyan Baya a Zaben Shugaban Kasa

 

Za a samu maslaha a jahar Nasarawa idan aka zo zaben dan takarar shugaban kasa na APC a cewar wani dan majalisar jahar.

Balarabe Abdullahi, kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa ya fadi hakan yayin ziyarar da masu zawarcin takarar.

Yahaya Bello suka kai masa Kakakin majalisar dokokin jahar Kogi tare da sauran mambobi sun ziyarci takwaran su na Nasarawa don neman takarar Yahaya Bello.

Nasarawa – Kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa Rt Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki a jahar za su hadu don daukar matsaya daya wajen zabar dan takarar shugaban kasa na 2023.

Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a zauren majalisar dokokin jahar Nasarawa lokacin da Rt Hon Mathew Kolawole, Kakakin Majalisar Jahar Kogi, ya jagoranci sauran membobin majalisarsa don kai masu ziyara game da neman takarar Shugaban kasa da Gwamna Yahaya Bello ke yi a 2023.

Abdullahi ya ce ‘yan jam’iyyar APC na majalisar dokokin jahar Nasarawa suna da kwarin gwiwa kan karfin Gwamna Bello na zama Shugaban Najeriya na gaba a 2023.

Ya kara da cewa a koyaushe majalisar tana magana da murya daya kuma za ta gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jahar domin daukar matsaya daya akan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

“Mun yarda da karfin Mai Girma Gwamna Yahaya Bello kasancewar shi mutum ne da ba ya wasa da batun rashin tsaro saboda ba za a sami ci gaba ba idan babu tsaro.

“Mun dauki wannan ziyarar a matsayin abun farin ciki. Mu a nan Majalisar Dokokin Jahar Nasarawa koyaushe muna magana da murya ɗaya kuma koyaushe muna tafiya ta hanya ɗaya.

“Muna son tabbatar muku cewa mu a Jahar Nasarawa za mu yi magana da murya daya kan batun shugabancin 2023.

“Muna da shugabannin da muka yi imani da su sosai. Za mu tattauna wannan ra’ayi naku da shugabanninmu don yin magana da murya daya,” ‘in ji Kakakin.

Kakakin majalisar yayi amfani da wannan dama wajen yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan irin ci gaban da ya samu a fadin jahohin tarayya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here