Guguwa: Mutane 9 Sun Rasa Rayukansu a Yankunan Iran da Oman

 

Aƙalla mutum 9 suka mutu sakamakon guguwa tafe da ruwan sama da wasu yankunan Iran da Oman.

Guguwar ta sauka a yankunan a jiya Lahadi, tafe da iska mai gudu kilomita 120 zuwa 150 cikin sa’a guda a cewar shaidu.

An kwashe dubban mutane daga yankunan da ke gabar ruwa a Oman da unguwanni birnin Muscat.

A Iran, mahukunta sun ce mutum shida suka mutu bayan a yankunan kudu maso gabshin Sistan-Baluchestan.

Gine-gine gwamnati da tittuna da tarukan wutar lantarki duk sun lalace.

A Oman mutum 3 suka mutu, ciki akwai yaro guda da ruwa ta tafi da shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here