Sheikh Gumi ya Bude wa Fulani Makiyaya Makaranta a Dazukan Jahar Kaduna

 

Rahotanni sun ce sanannen malamin addinin musuluncin nan a arewacin Najeriya Sheikh Ahmad Gumi, ya buda makaranta ga fulani makiyaya da ke zaune a dazukan jahar Kaduna.

Sheikh Gumi ya ce samar da irin wadannan ababe ga fulani makiyaya a dazukan da suke rayuwa zai taimaka wurin yakar akidoji marasa kyau.

Haka ma ya karyata maganar da ake yadawa da sunansa cewa Najeriya za ta shiga bala’i, matsawar ta ayyana yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Sheikh Ahmad Gumi ya saka wa makarantar tasa suna ‘Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio’.

Kuma wannan makaranta na zaune ne a garin Kagarko, a kusa da gandun dajin Kohoto da ke jihar ta Kaduna.

Jaridar Vanguard ta ambato shi yana cewa ” da za a samar da irin wannan cibiya ta ilmantar da fulani makiyaya a duka fadin Najeriya, to kuwa da al’umma sun samu zaman lafiya.” Inji Gumi.

Ya kara da cewa ” a maimakon kudaden da ake kashewa wurin sayen makamai da ake yakar yan bindigar, kamata yayi gwamnatin Najeriya ta yi amfani da kudin wurin gina musu makarantu da samar musu da malamai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here