Gwamnatin Tarayya za ta kwato fam 200m da Aka Sace Aka Boye a Kasar Amurka

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana yunkurinta na kwato wasu kudaden da aka sace su mallakin kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya ke tattaunawa a wani taro a Amurka.

Ya bayyana cewa, gwamnati na shirya wasu hanyoyi don tabbatar da kwato kudaden kasar nan cikin sauki.

New York, US – Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kwato fam miliyan 200 da aka sace aka boye a Amurka, yayin da gwamnatin ke shirin fara kwato kadarori mallakin kasar.

Yunkurin ya fito ne ta bakin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami wanda ke magana a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York ta kasar Amurka.

Channels Tv ta tattaro cewa, da yake magana kan yaki da cin hanci da rashawa da kwararar kudade a kasar, Malami ya ce:

duba yiwuwar dawo da fam miliyan 200 da wasu kari amma to, hakan ba yana nufin babu wasu kadarorin da ake alaka da su ba, dangane da sauran kasashen duniya da suka hada da Ireland.

“Muna bibiyar kadarori da yawa a duk fadin duniya sannan muna da niyyar shirya karin tarurrukan da suka shafi dawo da kudade a Burtaniya wanda ke da alaka da wasu mutane.”

AGF ya ce ba zai so ya kara bayyana dabarun da gwamnatin tarayya za ta bi wajen dawo da kudade ba, amma ya lura cewa:

“Gwamnati na kokarin tattara karfin duniya da ke da alaka da matakai da hanyoyi, dangane da saukake lamurra ga kasashe wajen dawo da kadarori cikin sauki.”

Ya kara da cewa gwamnati ta himmatu ga yakin da take yi da cin hanci da rashawa kuma ta hanyar fadada shimfida tarkon ta ga wadanda ke boye da kudaden da aka sace ko aka tsallakar.

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

‘Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta rawaito.

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Ya fadi haka ne lokacin da Babban Sakataren PIC ya bayyana a kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here