Gwamnan Gombe ya Koka da Matsalar Rashin Tsaro
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya magantu a kan matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar.
Yahaya ya bayyana cewa kasar bata taba riskar kanta a cikin irin wannan yanayi na rashin tsaro ba a tarihinta.
Ya kuma yi kira ga sabbin ciyamomin kananan hukumomin jihar da aka rantsar a kan su zamo masu gaskiya da amana.
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kasar Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta.
Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, a lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 11 a jihar.
Lamarin garkuwa da mutane da fashi da makami na ta karuwa a fadin kasar a yan baya bayan nan.
Gwamnan ya bukaci sabbin zababbun jami’an a kan su dauki tsaron rayukan jama’a da muhimmanci sosai, jaridar The Cable ta ruwaito..
Read Also:
“Kamar yadda duk kuka sani, Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta. Don haka ya zaman dole mu tanadi matakan da suka kamata domin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu,” in ji Yahaya.
“Ina kira ga sabbin ciyamomi a kan su tabbatar da dukkan matakan da aka tanada an aiwatar da su tare da dorewarsu don tabbatar da tsaro da lafiyar rayuka da dukiyoyin jama’a.
“A matsayinku na wakilan canji a matakin farko, ana sanya ran za ku hada kai da fata wajen tattara dabarun da za su yi aiki don ci gaba da sauya kananan hukumominku. Ina bukatarku da ku yi amfani da tarin kwarewarku don kawo ci gaba ga kananan hukumominmu da samar da damokradiyyar da ya kamata ga mutanenmu.”
Yahaya ya gargadi ciyamomin kan su tabbatar da sun rungumi gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu, inda yayi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci kowani irin launi na rashawa ba.
“Don haka, ya zama dole duk ku jajirce sannan ku tabbatar da gaskiya a wajen gudanar da ayyukanku. Ina umurtanku da ku zamo masu adalci da daidaito ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da banbancin siyasa ko al’ada ba. Ya zama dole a tabbatar da dorewar zaman lafiya da amanar da ke jihar,” in ji shi.