Harin Boko Haram: Gwamnan Borno ya Kai Ziyara ga Kauyukan da Harin ya Shafa
Yayinda ake ci gaba da yaki da ta’addanci, Boko Haram ta kai hari karamar hukumar Hawul a jihar Borno.
An kashe mutane uku, yayinda aka lalata ofishin yan sanda, shagunan kasuwa da sauran wurare a yayin harin.
Gwamnan jihar, Babagana Zulum, wanda ya kasance a wajen gari, ya takaita tafiyarsa sannan ya ziyarci garuruwan da abun ya shafa cikin gaggawa.
Zulum ya yi umurnin cewa a sake gina kadarorin da aka lalata sannan a samar da motocin fatrol.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba.
Gwamnan ya je Abuja don aiwatar da wasu jerin ayyuka amma sai ya takaita tafiyar sannan ya koma jiharsa a safiyar ranar Lahadi.
Read Also:
Harin na ranar Asabar ya shafi akalla garuruwa hudu da suka hada da Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro. Hatta ga makarantu, shaguna da wuraren bauta basu tsira ba a harin.
Yan ta’addan sun sace dubban buhuhunan kayan gona da manoma suka nome kwanan nan sannan suka debe kayayyaki a shaguna da kantunan kasuwa.
An kashe mutum uku a Shafa, biyu daga cikinsu sun kasance maharba da kuma dan farar hula daya.
Gwamna Zulum wanda ya zagaya don duba barnar da yan ta’addan suka yi ya yi umurnin cewa a sake ginasu a nan take.
Domin karfafa tsarin tsaro a garin Shafa, gwamnan ya bayar da umurnin samar da motocin fatrol shida da sauran kayayyakin amfani.
Ya kuma yi umurnin samar da motocin lura ga maharba da yan banga a Yamirshika.
Gwamnan ya kuma ce ya ziyarci garuruwan ne domin karfafa su da kuma samar da tallafi ga yan sa kai da ke ba hukumomin tsaro gudunmawa wajen dawo da zaman lafiya.
A cewarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kare rayuka da dawo da zaman lafiya a jihar Borno.