Jami’an Gwamnatin Ebonyi Sun Nemi da Gwamnan Jahar ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2023

 

Yan siyasan Najeriya sun fara shirye-shirye don zaben shugaban kasa na 2023.

Wasu jami’an gwamnatin jihar Ebonyi sun bayyana dalilin da yasa Gwamna Dave Umahi ya dace da takarar shugaban kasa.

Gwamnan ya fada ma mutanen kudu maso gabas abunda za su samu idan suka marawa APC baya.

An matsawa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi lamba a kan ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe da sauran mambobin majalisar dokokin jihar sun bukaci Umahi da ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an sun ziyarci gwamnan a mahaifarsa da ke Uburu, karamar hukumar Ohaozara don tattauna lamarin tare da shi.

Da yake magana a madadin sauran jami’an, mataimakin gwamnan ya ce sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) saboda Umahi.

Ya ce:

“A sanda ka sanar cewar lokaci yayi da za a tafi gaba, da yawa daga cikinmu muna ta jan kafa, muna ta son tattaunawa amma a karshe, sai muka yanke shawarar tafiya da kai.Dole in fada maka gaskiya cewa wasunmu basu so APC ba amma muka yanke shawarar komawa saboda kai.
Don haka, muna kaddamar da cewa dole ka tsaya takarar kujerar Shugaban kasa.”

Gwamnan, a martaninsa ya bukaci jami’an da su ci gaba da ba APC goyon baya. Ya ce jam’iyyar ta samar da wata kafa ga yan Igbo domin su kimanta kansu da kyau.

Sai dai Umahi bai bayyana ko zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here