2023: Gwamnan Jahar Jigawa ya yi Jawabi Kan APC

Rikicin cikin gida da ya kunno kai a jam’iyyar APC reshen jigawa na iya haddasa mata rasa jihar a 2023.

Wannan shine matsayar Gwamna Muhammadu Badaru a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba.

Sai dai, Badaru ya ce ba zai yi danasani ba idan hakan ya faru saboda ya kafu a bangaren kasuwanci.

Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru, a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, ya bayyana cewa tsawaita rikicin cikin gida a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar zai yi sanadiyar shan kayen jam’iyyar.

Harma, Gwamna Badaru ya bayyana cewa APC na iya rasa Jigawa a zaben 2023 idan har ba a dauki matakin gaggawa game da rikicin cikinta ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana cewa idan har abubuwa suka kai wannan matakin, toh ba zai yi danasani ba saboda ba zai rasa komai ba a matsayinsa na dan kasuwa.

Badaru ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar reshen jihar. Ya kuma yi kira dukkan mambobin jam’iyyar da su rungumi junansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here