Rashin Tsaro: Gwamnan Jahar Kano ya Soki Gwamnan Jahar Kaduna

 

 

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje, ya soki maganar da gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya yi akan rashin tsaron yankin arewa maso yamma.

Dama gwamna El-Rufai yace saboda rashin daukar matakan da suka dace da gwamnonin arewa maso yamma ne suke janyo hauhawar rashin tsaro a yankunan.

Yayin da RFI suke tattaunawa da Ganduje ya ce ba lallai El-Rufai ya fahimci kokarin da jami’an tsaro suke yi bisa umarnin gwamnonin yankinsu ba.

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya soki furucin da gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi akan matsalar rashin tsaron yankin arewa maso yamma, Punch ta wallafa.

Idan ba a manta ba gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce rashin jajircewar gwamnonin yankin arewa maso gabas ne ya sanya kullum rashin tsaro yake hauhawa a yankin.

Sai dai a wata hira da gidan rediyon faransa (RFI) suka yi da shi a Kano a ranar Alhamis, Ganduje ya ce El-Rufai ba zai taba fahimtar kokarin da gwamnoni suke yi ba na umartar jami’an tsaro.

A cewar Ganduje, an shawarci jami’an tsaron da suke jahar Kano, Kaduna da Bauchi da su hada karfi da karfe wurin duba dajin Falgore dake Tudun Wada da karamar hukumar Doguwa da suke jahar Kano.

“Batun rashin jajircewa bai taso ba saboda jami’an tsaro sun shawarci mu hadu da Kano, Kaduna da jahar Bauchi don mu ga yadda zamu kawar da ‘yan bindiga daga dajin Falgore.

“Na yarda da hakan amma gwamnonin jahar Kaduna da na Bauchi ba su je taron ba, sai dai suka turo wakilai.

“Akwai batun kudi. Gwamnatin jahar Kano, Kaduna da Bauchi sun tura kudadensu kuma ana sa ran hakan zai haifar da da mai ido. “Ga alamu gwamnan bai gane yadda matsalar tsaro ba saboda ko wacce jaha da yanayinta,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here