Gwamnati na Kokarin Kawar da Duk Wani Tashin Hankali ko Fitina – Shugaba Buhari

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki al’ummar Filato su rungumi zaman lafiya, tare da jaddada cewa gwamnatin na yin duk mai yiwuwa domin kawar da duk wani tashin hankali ko fitina.

Shugaban ya yi kiran ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu.

Sanarwar ta ce duk da irin kokarin da gwamnati take yi wajen tabbatuwar zaman lafiya dole sai malaman addinai da sarakuna da sauran shugabannin sun guji amfani da duk wani salo ko yada batutuwan da ka iya ingiza rikici.

Buhari ya ce akwai tarin matsalolin da kasar ke fama a yanzu kuma yana da muhimmanci ‘yan Najeriya da sauran kasashe su ke fahimtar irin kokarin da suke yi wajen kawar da duk wasu rigingimu a fadin kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here