Ya Kamata Gwamnati ta Samar da Runduna ta Musamman Don Kare Makarantu – Atiku Abubakar

 

Biyo bayan sace daliban wata makarantar sakandare a Zamfara, Atiku Abubakar ya yi martani.

Ya bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta samar da runduna ta musamman don kare makarantu.

Ya kuma bayyana kokensa kan yawaitar sace dalibai a yankunan Arewa maso yammacin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ba da shawarar kirkiro da sabuwar rundunar ‘yan sanda don kare makarantu daga hare-haren ‘yan bindiga a yankunan da lamarin tsaro yake kara ta’azzara.

Ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sace dalibai 73 da aka yi kwanan nan a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya dake Karamar Hukumar Maradun a Jahar Zamfara.

Tsohon dan takarar shugaban kasaN na jam’iyyar PDP ya kuma koka kan harin da sace daliban.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, Atiku ya bayyana cewa:

“Ina bakin ciki da rahotannin sake sace dalibai a Zamfara. Ga yankin da ke tasowa a fagen ilimi mai mahimmanci, ci gaba da kai hari kan ci gaban mu ba abin yarda bane.

“Watakila lokaci ya yi da za a kirkiri Sashin Jira da Kare Makarantu na musamman don kare makarantu a yankunan da ke fuskantar wadannan hare-hare.

“Idan ba mu dauki matakan riga-kafi ba, ina tsoron cewa ilimi a yankunan da suke dama a lalace na iya fuskantar asarar da ba za a iya gyara ta ba.

“A halin yanzu, ina fatan ana duk wani kokari da za a yi don ganin an dawo da daliban cikin hanzari.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here