Sukar Gwamnatin Buhari: Kungiyar Arewa ta Nemi da a Hunkunta Bishop Kukah

 

Matasan Arewa sun bi sahun sauran kungiyoyi don yin martani a kan furucin Bishop Kukah game da gwamnatin Shugaba Buhari.

Kungiyar matasan bata tsaya ga Allah-wadai da furucin malamin ba kadai, ta yi kira ga kama shi da kuma hukunta shi.

Bishop din na Katolika a Sokoto ya zargi gwamnatin Buhari da son kai da kuma gazawa.

A cewar kungiyar Arewan, furucin Kukah na tunzurawa ne da cin amanar kasar Najeriya.

Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta bayyana furucin Bishop Mathew Kukah na baya-bayan nan a matsayin kokarin karfafa yin juyin mulki.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Yerima Shettima, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba, zuwa ga Legit.ng, kungiyar ta ce hakan tayar da fitina ne kan zababbiyar gwamnatin damkradiyya ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku tuna cewa Kukah a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, ya zargi Shugaban kasa Buhari da son kai.

Da suke nuna rashin jin dadinsu kan furucin, AYCF ta ga laifin Kukah da yayi amfani da son kai a matsayin makamin bata kan gwamnati da mutanen Najeriya.

Kungiyar arewar na so a kama malamin sannan ya fuskanci hukunci kan abunda ta bayyana a matsayin cin amanar kasar Najeriya.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya Kukah cikin mutanen da za a dunga kula da duk wani motsinsu kan yunkurin kawo hargitsi a kasar ta hanyar hada kudu da arewa rigima.

Shettima a jawabin, ya bayyana abunda Kukah yayi a matsayin aikin shaidan a yayinda arewa ke fafutukar dawo da zaman lafiya da daidaita tsaro a yankin da Najeriya.

A cewarsa, a wannan lokaci, Najeriya na bukatar shawara mai kyau da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ba wai furucin da zai tunzura matsalolin kasar ba.

A gefe guda, mun ji cewa Kukah, ya sha caccaka kan sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi a sakonsa na Kirsimeti.

Kungiyar dattawa arewa ta NEF ta ga laifin malamin kan cewa da yayi a tsige Shugaban kasar ta tsarin da baya bisa damokradiyya.

Kukah a martaninsa kan hare-hare da kasha kashe da ake yi a kasar, ya ce idan da Musulmin da ba dan arewa bane Shugaban kasa sannan ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi juyin mulki da dadewa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here