Gwamnatin Jihar Kano ta Fara Rushe Gine-Gine da ta ce an yi ba Bisa ƙa’ida ba

 

Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara rushe wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne bayar da umarnin fara rushe gine-ginen waɗanda ya ce an yi su ba bisa ƙa’ida ba a wasu wurare mallakar gwamnatin jihar.

Da safiyar ranar Asabar ne aka fara rusa wasu gine-gine a filin sukuwa a birnin domin ƙwato filin gwamnati kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Idan za a iya tunawa a alƙawuran yaƙin neman zaɓe da gwamnan ya yi, ya alƙawarta ƙwato filaye mallakar gwamnati da aka gina ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamnan ya ce za a rusa wuraren da aka gina a filayen makarantu da masallatai da filayen wasanni, da maƙabartu da kasuwanni da asibitoci, domin tabbatar da bin tsarin ginin birnin, tare da ƙawata shi da kuma tsare lafiyar al’ummar jihar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su yi haƙuri, kasancewar sabuwar gwamnatin jihar na son tabbatar da ci gaban jihar.

Dama dai a jawabin da sabon gwamnan jihar ya yi bayan shan ranstuwar kama aiki ranar Litinin, ya bayar da umarni ga jami’an tsaro a jihar da su ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da ya ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sayar wa wasu mutane a jihar.

A ranar Juma’a ne gwamnan ya bayar da umarni ga masu gine-gine a filin da ke bayan sansanin alhazai ( Hajj Camp) a jihar da su gaggauta dakatar da ginin nasu, bayan wata ziyara da ya kai wajen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here