Gwamnantin Jahar Kwara ta Sallami Kwamishinoninta

Gwamnan Kwara ya bada sanarwar ya sallami Kwamishinonin da ya nada.

Hadimin Gwamnan ya bada sanarwa, ya ce SSG kadai ya tsallake sallamar.

AbdulRahman AbdulRazaq ya godewa mukarraban da su ka yi masa hidima.

Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sauke dukkanin mukarrabansa.
Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto ranar Litinin.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar da jawabi ta bakin babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya na mai bada wannan sanarwar.

Kamar yadda Mista Rafiu Ajakaye ya bayyana, sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Mamman Jubril ne kadai gwamna ya bari a kan mukaminsa.

A wannan babbar kakkaba da gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi a ranar Lahadi, Mamman Jubril ne kurum wanda ya tsira da kujerarsa.

Ajakaye ya ce gwamna ya ba kwamishinonin da aka sauke umarnin su sallamawa manyan jami’an da ke ma’aikatunsu duk wasu aiki da ake kai.

Gwamna AbdulRazaq ya godewa duk wadanda ya yi aiki na tsawon kusan shekara daya da rabi.

Sanarwar ta ce: “Mai girma gwamna ya yi godiya ta musamman ga mukarrabansa saboda irin gudumuwar da su ka bada wajen cigaban jihar.”

Ajakaye ya cigaba da cewa: “Gwamna ya na yi masu fatan alheri a ayyukan da za su sa a gaba.”

Sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar ya bayyana cewa aikin kwamishinonin jihar ya kare ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here