Gwamnatin Tarayya Zata Rage Harajin Motoci – Hameed Ali
A shekarar 2019 ne shugaban hukumar kwatsan, Hameed Ali, ya shawarci gwamnati ta rage harajin shigo da motoci.
Hameed Ali ya ce kara farashin da gwamnati ta yi ya sace gwuiwar masu sana’ar sayar da motoci tare da kara yawan matsalar fasa kwauri.
Yanzu haka, gwamnati tarayya ta sanar da cewa ta kammala dukkan tsare-tsare domin zabtare harajin motoci Gwamnatin tarayya ta gama kammala tsare tsare don ganin ta zabge harajin motocin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje daga kaso 35% zuwa kaso 30%.
Wannan na cikin ƙunshin ƙudiran shekarar 2020 da ma’aikatar kuɗi za ta gabatarwa majalisar dattijai, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Ƙudirin zai zamo doka da zarar ƴan majalisu da Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, sun amince da shirin.
Bayanan ƙudirin, wanda fadar shugaban ƙasa ta watsa, ya nuna cewar harajin Tan-Tan, manyan motocin dakon kaya, da sauran motocin aikin gona, za’a zabge su daga kaso 35% zuwa kaso 10%.
Read Also:
Tsarin ya ɗauke biyan haraji ga kamfanonin da suka bada gudunmawar tallafin annobar COVID-19 a ƙarƙashin inuwar kamfanoni masu zaman kansu da ke yaƙi da annobar Korona (CACOVID).
Domin rage raɗaɗi da kawo sauƙin kasuwanci, kudirin ya kawo shawara mallakar manhaja a matsayin kuɗaɗen da aka kashe wajen gudanar da kasuwanci.
Zainab Ahmad, ministar kuɗi, kasafi da tsare tsare, a baya baya nan ta yi bayani kan yadda za’a zabge harajin shigo da kayayyaki don ragewa da sauƙaka kuɗin tafiye tafiye.
“Dalili da manufar yin hakan shine mu rage tsadar kuɗin tafiye tafiye, wanda jigo ne wajen haifar da hauhawar farashin kayayyaki” Zainab ta faɗawa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala wani taron ƙusoshin gwamnati a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.
A shekarar 2019, Hameed Ali, shugaban hukumar Kwastam ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta rage harajin da ake biya akan motocin da ake shigowa dasu zuwa kaso 10%.
A wancan lokacin, Hameed Ali, ya yi gardamar cewa yawan harajin da ake biya ƙari akan kaso 35% ya sacewa masu shigo da motocin guiwa, wanda ya jawo suke shigo da motocin zuwa maƙwabtan ƙasashe domin su yi fasa ƙwaurinsu.