Allurar Rigakafin Corona: Gwamnatin Tarayya na Shirin Kashe Sama da N396bn

 

Gwamnatin za ta kashe kudaden da suka haura Naira biliyan 396 a cikin shekarun 2021 da 2022.

Gwamnati ta kuma bayyana cewa, ana iya samun ragakafin sakamakon tallafi da ake samu daga kamfanoni masu zaman kansu Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ta kara da cewa Ma’aikatar Lafiya na aiki kan cikakkun bayanai game da gibin da za a bukaci Gwamnatin Tarayya ta cika a aikin yin allurar rigakafin.

Ta kuma bayyana cewa girman kasafin kudin da aka gabatar wanda bangaren zartarwa da bangaren majalisa suka amince dashi har yanzu ba a warware shi ba, saboda Ma’aikatar Tsaro da Lafiya, har yanzu ba ta ba da cikakken bayani game da kayan aikin sojan ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here