Gwamnatin Tarayya Zata Bada Makudan Kudade Don Gyara Tituna da Filin Jirgin Sama
Gwamnatin Tarayya za ta gyara titin da ya hada Kaduna da Jihar Filato.
Za kuma ce ayi aikin hanyar Yakassai-Badume-Damargu-Makinzali a Kano.
Hadi Sirika ya ce Gwamnati za ta fadada filin jirgin sama na jihar Borno.
A ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, 2020, majalisar FEC ta amince da bukatar batar da N59.35 wajen gyaran hanyoyi da aikin filin jirgin sama.
Jaridar Vanguard ta ce Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya gabatar da takardun kwangila na aikin N50.858bn da yake so a duba.
A zaman da aka yi jiya, FEC ta yi na’am da wannan bukata na gyaran titi a jihar Kano kuma aikin hanyar Kano zuwa Filato wanda za scu ci N50bn.
Read Also:
Majalisar zartarwar kasar ta yarda a ba kamfanin CCECC aikin gina titin Yakassai-Badume-Damargu-Makinzali a jihar Kano a kan kudi N12.157bn.
Haka zalika kamfanin Setraco Nigeria Limited za su gyara hanyar Kaduna-Panbegua-Jos. Wannan katafaren aiki zai ci gwamnatin tarayya N38.701bn.
Shi ma Ministan birnin tarayya, Mallam Mohammed Bello, ya samu an amince da wasu tituna biyu da yake so ya yi a Abuja; Yaba-Kpahe da na Kwali/Abaji.
Rahoton ya nuna Ministocin sun kuma sake duba kudin da za a kashe wajen gyara titin Ring Road III zuwa Rind Road IV har zuwa Abuja industrial Park.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a madadin Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika, ya ce an yarda a fadada filin jirgi na Maiduguri.
Fadada filin sauka da tashin jirgin saman zai ci N719, 117, 868.60. Kamfanin Luvaslink Projects Limited za su yi aikin kamar yadda Lai Mohammed ya fada.