Wasu Gwamnonin Sun Shiga Ganawa da Gwamnan Katsina

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun yi ganawar sirri.

SUn samu ganwa da gwamnan jihar Masari, Aminu Masari a gidan gwamnatinsa a kan yawaitar satar jama’a.

Gwamna Kayode ya ce tsanantar rashin tsaro a yankin arewa maso yamma da kasar nan tana tada musu hankali.

Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga ganawar sirri.da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yawaitar garkuwa da jama’a.

Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi bayani ga manema labarai bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Katsina.

Ya yi kira ga takwarorinsa da su dauka salon da za su sa matasa su gujewa aikata laifuka, jaridar The Punch ta wallafa.

Gwamnan jihar Ekitin ya ce shi da takwarorinsa duk sun damu da halin da tsaron arewa maso yamma da dukkan kasar nan ke ciki.

Fayemi ya yi kira ga dukkan takwarotinsa da su tsananta yaki da ‘yan bindiga da dukkan laifuka da suka addabi yankin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here