2023: Zaku Iya Haɗa Kanku ku Yaƙi jam’iyya Mai Mulki Matuƙar Baku Gamsu da Salon Mulkinta ba – Gwamnan Ekiti ga Matasa

 

Shekaru kaɗan suka rage babban zaɓen 2023 ya iso amma gwamna Fayemi ya shawarci matasa su fara aiki tun kafin zuwan zaɓen.

Gwamnan Ekiti yace maimakon damuwa da yawan ƙorafi, duk wadanda basa goyon bayan mulkin APC zasu iya haɗa kansu su kawar da ita a zaɓe mai zuwa.

Jigon jam’iyyar APC ɗin ya kuma yi magana a kan ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama dashi, yace akwai buƙatar a zauna a sake gyara tsarin tsaro gaba ɗaya.

Gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi, yace Duk wanda baya jin dadin salon wannan mulkin ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC, yana da damar da zai canza a babban zabe mai zuwa.

Gwamnan ya baiwa matasan ƙasar nan shawara, yace zasu iya haɗa kansu su yaƙi jam’iyya mai mulki matuƙar basu gamsu da salon mulkinta ba.

Fayemi yace maimakon ƙorafin da suke yi sabida yanayin da ƙasar ke ciki, kamata yayi matasan su fara ƙoƙari tun yanzu suyi amfani da damarsu da demokaraɗiyya ta basu, su canza APC idan hakan suke buƙata.

Gwamnan wanda jagora ne a jam’iyyar APC, yayi wannan jawabi ne a ranar 1 ga watan Mayu, yayin da yake jawabi a wani shiri da cibiyar kiristoci ke shiryawa duk shekara mai suna ‘The Platform’ a Iganmu, jahar Lagos.

Gwamnan yace:

“Wani zaɓen zai zo nan gaba, idan baku gamsu da abinda APC keyi ba, ku haɗa kanku, ku daina yawan ƙorafe-ƙorafe, ku shirya yaƙar jam’iyyar, ku nemi haɗin kan mutane waɗanda suma suke shirya hakan, ku fitar da jam’iyyar APC daga mulki.”

“Kuna da cikakkiyar damar yin haka, ku zaɓi waɗanda kuke ganin zasu yi abinda ya dace, bawai kuzo kuna ƙirƙirar wani abu mara tsari ba.”

A wani rahoton da Legit.ng ta tattaro, gwamnan yace akwai buƙatar a canza gaba ɗaya tsarin da ake amfani dashi wajen yaƙar yan ta’adda.

Fayemi ya bayyana cewa tsarin tsaron ƙasar nan da ake tafiya akansa a yanzun, bazai haifar da ɗa mai ido ba.

“A wannan lokacin ku yi kira a gyara gaba ɗaya tsarin tsaron ƙasar nan.” Gwamnan ya baiwa matasa shawara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here