APC Reshen Zamfara ta Musanta Rahoton Dake Cewa Manyan Hadiman Gwamna Matawalle Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

 

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta karyata rahoton da ke cewa manyan hadiman Matawalle ne suka koma PDP.

A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta yi ikirarin cewa mashawartan Matawalle uku sun sauya sheka daga APC.

Kakakin APC a Jihar, Yusuf Idris, ya fito ya fayyace gaskiya tare da bayar da hujjoji kan wadanda suka koma PDP.

Zamfara – Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta musanta rahoton dake yawo cewa manyan hadiman gwamnan Bello Matawalle guda uku sun sauya sheka zuwa PDP.

APC ta bayyana cewa rahoton wanda yan midiyan gidan PDP suka kirkira cewa mashawarta na musamman uku da Matawalle ke ji da su sun bar APC karya ne.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa a wasu sanarwa biyu daban-daban da PDP ta fitar, ta ce makusantan gwamnan ba su gamsu da salon mulkin Matawalle ba shiyasa suka kama gabansu.

“Tsohon shugaban APC a Zamfara, mataimakin sakataren tsare-tsare na APC a shiyyar Zamfara ta tsakiya, Alhaji Musa Malalla sun koma PDP don marawa Dauda Lawal baya,” inji PDP.

Wata sanarwan ta daban ta ce:

“Guguwar sauya sheka ta turnuke APC mai mulki a Zamfara yayin da masu baiwa gwamna shawara na musamma har guda uku suka koma PDP. Dan takarar Gwamna, Dauda Lawal ne ya karbe su a gidansa.”

Karya ce tsanta inji APC

A ruwayar Punch, yayin da take martani, jam’iyyar APC ta bakin mai magana da yawunta, Yusuf Idris, ya ce wadan da suka sauya shekar ba su da kusanci da gwamna Matawalle.

Yace mutanen guda uku, Hamisu Magami, Abubakar Maigandi da Yunusa Rosy, sun rike mukamin ne a mulkin tsohon gwamna, Abdul’aziz Yari.

Idris ya kara da cewa Garba Muhammad Danburan, tsohon shugaban hukumar zabe ta jiha (ZASIEC) ne amma ba shugaba mai ci ba kamar yadda PDP ta yi ikirari.

Kakakin APC ya bayyana rahoton da gurbatacce kuma karya ce mara tushe. Idris ya ce:

“Rahoton baki ɗayansa gurbatacce ne kuma wani shiri ne da PDP ta kirkiro tare da masu sauya shekan na rufa-rufan kanzon kurege. Yana da kyau mu share waswasin yan Najeriya domin Zamfarawa sun san komai.”

“Mutane ukun da aka ce hadiman gwamna ne karya ne. Sun rike mukaman masahawarta ne a zamanin mulkin tsohon gwamna, Abdul’Aziz Yari. Ba su da gurbi a mulkin Matawalle.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here