Rabiu Kwankwaso: Hadimin Ganduje ya Bawa Tsohon Gwamna Hakuri

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta damki Alibaba, mai baiwa gwamnan Kano shawarwari a kan harkar addini.

Ta zargi Alibaba da jingina wa Kwankwaso mallakar Kamfanin Dangote Oil a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo.

Da kyar aka bayar da belinsa bisa sharadin komawa gidan rediyon ya karyata kansa da kansa, kuma sai da yayi hakan.

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta damki Ali Muhammad Alibaba, mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara na musamman a kan harkokin addini, bisa ikirarin da yayi a kan Rabiu Kwankwaso.

Ali Baba ya ce Aliko Oil Company Limited mallakin Kwankwaso ne a wata hira da aka yi dashi a wani gidan radiyo.

A tattaunawar, Alibaba ya bukaci Kwankwaso ya fito fili yayi rantsuwa a kan cewa ba kamfaninshi bane. A cewar Alibaba, kalar kamfanin ja da fari ne, kuma hakan yayi kama da kalar da kwankwaso yake amfani da ita a siyasarsa.

Ma’aikatan Aliko Oil sun hassala da wannan magana tashi, sai suka kai karar Alibaba hedkwatar ‘yan sanda ta Kano da ke Bompai.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai a kan yadda ‘yan sanda suka gayyaci Alibaba don ya amsa tambayoyinsu, sai kuma suka rike shi.

Bayan kwashe sa’o’i suna tambayarsa, sai suka bayar da belinsa, da sharadin zai koma har gidan rediyon da yayi maganganun ya karyata kansa.

A ranar Asabar, Alibaba ya bayyana a shirin gidan rediyon, ya baiwa kamfanin hakuri bisa alakantasu da tsohon gwamnan da yayi.

Da aka tambayi kakakin ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, cewa yayi ba shi da labari a kan faruwar lamarin, saboda yayi tafiyar ‘yan kwanaki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here