Hadimin Sarki Ya Maida Martani Akan Dakatar da Fansho da Gwamnatin Kwara ta yi
Matakin na zuwa ne biyo bayan daukar irin matakin da Jihar Legas tace zata yi.
Mai magana da yawun Saraki ya ce wata 33 kenan da tsohon gwamna Abdulfatah Ahmed ya dakatar da biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni.
Ya bukaci gwamnati ta dinga bincike kafin ta kwaikwayo wata jihar don kauracewa abin kunya.
Wani hadimin tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, ya soki gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, kan wani alkawarin karya dokar da ta tabbatar da biyan tsofaffin gwamnoni fansho tsahon rayuwarsu dama wasu hakkoki su da mataimakansu.
Abdulrazaq ya yi alkawarin yin watsi da dokar biyan fanshon kwanaki kadan bayan gwamnan Lagos, Babajide Sanwa-Olu, ya yi alkawarin mika kudirin gaban majalisa akan irin wannan doka a jihar.
Sai dai, Abdulganiyu Abdulqadir, mai magana da yawun Saraki, a harkokin cikin gida, ya ce an karya dokar tun 2018 kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Read Also:
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Abdulqadir ya shawarci gwamnatin Jihar Kwara da ta dinga bincike kan al’amura kafin kwaikwayo wata jihar don kauracewa abin kunya.
Ya ce tsohon gwamna Abdulfatah Ahmed ya dakatar da biyan fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu tun watan Fabarairun 2018, watanni 33 da suka gabata.
Abdulqadir ya ce, “abin damuwa ne yadda aka shigo da siyasa cikin hukuncin da gwamnati karkashin jagorancin Abdulrahman Abdulrazaq kuma ya zama babban abin da ake batu a tsakanin yan siyasa, ba tare da la’akari da irin abun kunyar da zai janyo al’ummar jihar ba.
“Idan za a iya tunawa a Fabrairun 2018, majalisar dokokin jihar Kwara ta yi wa dokar kwaskwarima kuma ta rushe biyan tsofaffin gwamnoni fansho, abin da ya samu yabo daga shugaban majalisar dattawa na waccan lokacin, Dr Bukola Saraki.”
Abdulrazaq ya bayyana a ranar Juma’a cewa zai dauki mataki akan dokar da ta baiwa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu damar samun fansho a Jihar.
Abdulrazaq, ta bakin Sakataren watsa labarai, Rafiu Ajakaye, ranar Juma’a, ya ce zai mika kuduri a gaban majalisa don warware dokar.