Kano: Matar da ta Haifi ‘ya’ya 5 ta Rasu

 

Hafsatu Yusuf, matar da Legit Hausa ta ruwaito ta haifi ‘yan biyar a asibitin Murtala dake birnin Kano ta rasu sakamakon zubar jini.

An gudanar da jana’izar marigayiyar a unguwar Hotoro yayin da jariranta biyar suke karkashin kulawar likitoci ta musamman a asibiti.

Ma’aikatar lafiya yi kira ga al’umma da su tallafa wa jariran da madara da tufafi don ci gaba da kula da su bayan rasuwar Hafsatu.

Kano – Cikin kankanin lokaci bayan samun labarin farin ciki na haihuwar jarirai biyar rigis, labari mai taba zuciya ya riski al’ummar jihar Kano na rasuwar mahaifiyar jariran, Hafsatu Yusuf.

Kakakin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya tabbatar da cewa Hafsatu ta rasu ne da misalin karfe 2:00 na dare a yau Alhamis, 26 ga Maris, 2026.

Kano: Matar da ta haifi ‘ya’ya 5 ta rasu

Kofar Na’isa ya bayyana cewa Hafsatu ta fuskanci matsalar zubar jini mai tsanani bayan ta haifi jariran — maza uku da mata biyu, a cewar rahoton Punch.

Duk da kokarin da kwararrun likitoci suka yi a asibitin Murtala domin ceto rayuwarta, abin ya faskara. Ya ce:

“Ta sha fama da zubar jini tun bayan haihuwar, kuma duk kokarin likitoci na ganin an shawo kan lamarin ya ci tura.”

Tuni dai aka gudanar da jana’izar marigayiya Hafsatu Yusuf kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidansu dake unguwar Hotoro a birnin Kano.

An nemi tallafin jama’a kan ‘ya’yan Hafsatu Wannan babban rashi ya girgiza al’ummar jihar, musamman duba da yadda aka yi ta murna da wannan haihuwa ta daban a jiya Laraba, in ji rahoton Vanguard.

A bangare guda, hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa jarirai biyar din suna cikin koshin lafiya kuma suna karkashin kulawar likitoci ta musamman a asibiti.

Ma’aikatar lafiyar ta yi kira ga jama’a da su kawo tallafin madara da sauran muhimman abubuwan bukata ga jariran.

“Muna rokon jama’a da su taimaka wa jariran da madara da sauran muhimman abubuwan bukata.”

– Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa.

Mijin matar, Salisu ya yi martani

Wani abin lura shi ne cewa sakamakon binciken na’urar hoton ciki na farko ya nuna cewa ‘yan uku ne Hafsatu za ta haifa, amma yayin da nakuda ta tsananta, sai aka samu karin wasu jariran biyu, wanda hakan ya zama ‘yan biyar.

Malam Salisu Nafiu, mijin marigayiyar wanda matukin Keke-Napep ne, ya nuna tsananin alhini kan wannan rashi, ko da yake ya gode wa gwamnatin jihar Kano bisa alkawarin daukar nauyin kulawa da jariran da ta yi.

Gwamnatin ta sake jaddada aniyarta ta yaki da mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, duk da cewa wannan rashi ya faru ne kwanaki kalilan bayan kaddamar da shirin tallafa musu.

“Akwai rawar da za mu taka” – Sanusi II

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a yi amfani da tsarin gargajiya wajen magance mace-macen mata masu juna biyu.

Ya yi nuni da cewa dole ne a fifita kula da mata da yara, yana mai cewa matsalar mutuwar mata masu ciki da jarirai tana da alaka da sakaci.

A cewar Sarki Sanusi II, ana iya rage wannan matsaloli na mutuwar mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar daukar matakan kulawa da samar da abinci mai kyau.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here