Hajiya Imaan Suleiman Ibrahim: Shugaba Buhari ya Nada ta a Matsatin Sabuwar Shugabar Hukumar NAPTIP

Shugaban kasa ya yi nadi mai muhimmanci a ma’aikatar hana safarar mutane.

Najeriya na fama da matsalan safarar mutane zuwa kasashen waje domin bauta da karuwanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabuwar shugabar hukumar dakile mutane watau NAPTIP.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Ya bayyana cewa gabanin nadinta ta kasance babbar mai bada shawara ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, kan sadarwa.

Imaan za ta maye gurbin Julie Okah-Donli wacce Buhari ya nada tun shekarar 2017.

Yace: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Imaan Sulaiman-Ibrahim matsayin sabuwar dirakta janar na hukumar NAPTIP.”

“Mrs Sulaiman Ibrahim ‘yar asalin jihar Nasarawa ce kuma ta karanci Sociology a jami’a sanan tayi digir-gir a kasuwanci.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here