Hajji 2021: Jahar Kano Zata Mayar wa da Maniyyata Kudadensu

 

Jahar Kano ta yi kira ga maniyyata aikin Hajjin 2021 su zo su karbi kudaden da suka biya.

Wannan na zuwa ne watanni bayan gudanar da aikin Hajjin ba tare da karbar ‘yan wata kasa ba.

Hukumar jin dadin Alhazai a jahar ta bayyana adadin mutanen da suka biya kudadensu na Hajji.

Kano – Hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Kano (KSPWB), ta ce za ta mayar wa maniyyata 2,300 da suka ajiye kudin aikin hajjin 2021 kudaden su da suka ajiye.

Gwamnatin Saudiyya a ranar 12 ga watan Yuni, ta ba da sanarwar cewa alhazan kasashen waje ba za su samu damar yin aikin Hajjin 2021 ba, tare da takaita aikin hajjin ga ‘yan kasar da mazauna cikinta.

Mahajjata 60,000 suka yi aikin Hajji a 2021 saboda cutar ta Korona, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Matakin jahar Kano game da maniyyata aikin Hajjin 2021 Babban Sakataren Hukumar ta KSPWB, Alhaji Muhammad Abba ya bayyana nufin mayar da kudaden ga maniyyata a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba 18 ga watan Agusta, 2021 a jahar Kano.

Legit Hausa ta tattaro daga News Diary in da Abba ya ce maniyyata 5,500 ne suka yi rajistar aikin Hajjin 2021 a jahar.

A cewarsa:

“Sama da ceki 200 a shirye amma masu su ba su zo ba, muna kuma sarrafa karin ceki din.”

Abba ya yi kira ga sauran maniyyatan da ke son karbar kudinsu da su rubuto a rubuce, domin a ba da ceki kudinsu.

NAN ta ba da rahoton cewa a shekarar 2020, mahajjata 1,000 ne aka ba su izinin yin aikin hajji saboda Korona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here