Halin da Muke Ciki Zaɓi ne na Shugabanni da Mabiya – Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasa, ya yi kira ga ‘yan Nigeria a kan su daina dora alhakin matsalolin kasa a kan Allah.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a matsayin martani a kan kalaman shugaba Buhari a sakonsa na shiga sabuwar shekara.

A cewar tsohon shugabar, bai yarda Allah ne ya kaddara halin talauci da Nigeria ke ciki ba.

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi aiki tukuru tare da yin addu’a domin samun nasarar ƙasar nan a sabuwar shekara mai kamawa, kamar yadda today.ng ta rawaito.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Obasanjo ya nuna ƙin amincewarsa cewa, Allah ne ya ƙaddara halin talauci da Najeriya ke ciki, inda ya dora alhakin hakan ga shugabannin da suka jefa ta cikin wannan mayuwacin halin.

A cewarsa, “Bai kamata mu rinka dorawa Allah laifin halin da ƙasar mu ke ciki ba, dole mu zargi kanmu, Najeriya bai kamata ta zama talaka ba, bai kamata ɗan Najeriya ya kwanta da yunwa ba”.

“Halin da muke ciki zaɓi ne na shugabanni da mabiya. Addu’ata shine Ubangiji Ya sa shekarar 2021 ta zame mana alheri ga kowa, amma haka ba zai faru ba sai mun haɗa da aiki tukuru”.

Ya sake jaddada bukatarsa ga yan Najeriya cewa matuƙar suna son tabbatar Najeriyar da suke so, wajibi ne su tashi aiki tukuru sannan su haɗa da addu’a, don tunkarar kalubalen dake gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here