Kungiyar Matasan  Arewa Sun Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Haramta Haska Shirin BBNaija

 

Kungiyar matasa a Arewa ta yi kira ga gwamnati da babban murya.

Shirin BBNaija wani shiri ne da ake tara gardawa maza da mata ajanabai kulle cikin wani gida na tsawon watanni.

Ana zabge mutane daya bayan daya har mutumin karshe wanda shi zai lashe kyautar kimanin milyan 60m.

Wata kungiyar bada shawara ta matasa a Arewacin Najeriya (AYCF), ta yi ga gwamnatin tarayya ta haramta haska shirin BBNaija da akeyi a tauraron DSTV.

Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a, PT ta ruwaito Daily Trust.

Ya siffanta wannan shiri a matsayin Fitina ga al’umma.

Ya ce bai kamata gwamnati ta bari ana haska irin wannan shiri ba saboda yana koyar da badala da bayyana tsiraici.

Yace:

“Wannan a gani na fitina ne; bana son BBNaija kuma ban tunanin ya dace saboda rashin tarbiyya ne.

Bai kamata ana goya bayan irin wannan ba.”

“Na dade ina fadi ya kamata gwamnatin Najeriya ta haramta, bai kamata ana haskawa a kasarmu ba.”

“Kun ga, mutane da yawa na kallo don su ga tsiraici.”

An dade ana kira ga gwamnati ta haramta.

Wannan ba shi bane karo na farko da za’a yi kira ga gwamnati ta haramta haska BBNaija ba.

Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC), Kungiyar cigaban jama’a, gidauniyar raya al’adar Afrika da kungiyar iyaye mata, a baya sun bukaci haramta haska wannan shiri.

Wadannan kungiyoyin sun shigar da Kamfanin MutiChoice Nigeria Limited, Hukumar lura da ayyukan gidajen talabijin da rediyo NBC, da gwamnatin tarayya babban kotun tarayya dake Legas.

Bayan haka, Babban Faston Anglican Church of the Epiphany, Ifeanyi Akunna, shima ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta haramta shirin BBNaija da ire-irensa a Najeriya.

Ya ce cigaba da haska wannan shirin zai gurbata tarbiyyan matasan Najeriya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here