Ramadana: An Haramta wa Limamai Karanta Ƙur’ani Daga Wayar Hannu a Lokacin Sallolin Dare
Ma’aikatar waƙafi da harkokin addinin Musulunci ta Kuwait ta haramta wa limamai karanta Alƙur’ani daga wayoyinsu na hannu a lokutan nafilfilun dare na watan Ramadana.
Read Also:
Jaridar Al Rai ta ruwaito cewa bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun ƙaramin minista mai kula da harkar masallatai, Salah Al Shilahi.
Sanarwar ta ƙarfafa wa limamai gwiwa da su riƙa amfani da haddarsu ta Ƙur’ani a lokutan sallolin Tarawihi da Tahajjud, kasancewar su (limaman) misali ne ga sauran al’umma.
Ta ƙara da cewa ya kamata kowane limami ya yi muraji’ar karatunsa yadda ya kamata gabanin jan sallah a maimakon karantowa daga cikin waya.