An Samu Sautin Harbe-Harben Bindiga a Hanyar Enugu Zuwa Abakaliki

 

A halin yanzu tashin hankula tare da neman hanyar tsira ya cika babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki.

Masu ababen hawa a halin yanzu sun tsaya cak inda wasu ke neman mafaka sakamakon harbe-harben dake tashi.

Rundunar ‘yan sandan jahar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma tace jami’ai suna kan hanyar zuwa wurin Rahotanni daga jaridar The Nation sun nuna cewa ababen hawa da fasinjoji dake kan babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki sun tsaya sakamakon harbe-harben dake tashi a yankin Ezilo.

Kamar yadda tahotanni suna nuna, har yanzu ba a san abinda ya kawo harbe-harben ba.

An gano cewa, an kashe wasu mutum biyu a sabon rikicin iyaka da aka yi tsakanin yankunan Ezilo da Iyionu dake karamar hukumar Ishielu ta jahar.

Ba a tabbatar da cewa ko harbe-harben yana da alaka da rikicin iyakar da ake yi ba.

Wani fasinja mai suna Afam Cyprian, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Enugu, yace:

“Matafiya da yawa na neman wata hanya. Wasu sun koma kan hanyar Afikpo. Ina neman hanyar komawa Abakaliki.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tace kwamishinan ‘yan sandan jahar Ebonyi, Aliyu Garba, ya tura jami’an sintiri domin tabbatar da zaman lafiya tare da buda hanyar.

Amma kuma tace harbe-harben basu da alaka da rikicin yankin da aka fara tunda dama basu kusa da babbar hanya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here