Harbe Kanin Sowore: 1 Daga Cikin Mutane 5 da Masu Garkuwa Suka Sace ta Bayyana Yadda ta Gudu Daga Wurin su

 

Reverend Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna sheke kanin Sowore, ta bayyana yadda ta tsere daga wurin su.

Ayanwu ta bayyana yadda ta ke hanyar ta zuwa jahar Imo sai suka tsayar da su a jahar Legas, inda ta hau motar da za ta kai ta, babbar matsalar ta faru ne bayan motar ta lalace.

Ta bayyana yadda ta tsere ofishin ‘yan sanda cikin gaggawa a lokacin da ta ga hankalin masu garkuwa da mutanen ya karkata a kan wasu mutanen da suka sata.

Edo – Reverend Sister Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna kashe kanin Omoyele Sowore, kanin mai Sahara Reporters, ta bayyana yadda ta tsere daga hannun su.

Daily Trust ta rawaito cewa, sun harbe kanin Sowore har lahira ya na hanyarsa ta zuwa jami’ar Igbinedion Okada da ke jahar Edo a ranar Asabar.

Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, sun harbe shi ne yayin da ya yi yunkurin tserewa daga masu garkuwa da mutanen da ke kan titin Benin zuwa Legas.

Ayanwu wacce ke tafe da kariyar Ubangiji ta bayyana yadda ta ke hanyarta ta zuwa jahar Imo sai ta tsaya a Legas inda ta hau motar da za ta kai ta.

A cewarta, matsalar ta auku ne lokacin da motar ta samu matsala, Daily Trust ta wallafa.

Ta bayyana yadda ta shige ofishin ‘yan sanda bayan ta ga hankalin masu garkuwa da mutanen ya karkata daga kan ta.

“Ana ruwan sama da misalin karfe 7:30 na dare sai suka turo wata mota ta dauke mu a daji. Suka amshi wayar mutumin da sauran abubuwa.

“Sai na lura da cewa hankalinsu ya karkata a kan mutumin, sai na cire kyallen da suka rufe min ido da shi na lallaba na gudu ba tare da sun lura ba.

“Bayan na isa kan titi sai na hadu da wani mutum da ya nuna min wasu ‘yan sanda a bakin titin masu babura bayan na bashi labari na.”

Daga nan ne suka kai ni ofishin su da ke Benin, babban birnin jahar Edo.

Batun yadda suka sace ta tace:

“Maza 5 ne suka bayyana daga cikin daji bayan motar mu ta samu matsala suka fara harbe-harbe.”

Ta ce, take a nan suka zagaye su sannan suka umarci kowa ya fito daga abin hawansa kuma ya kwanta sannan suka rufe musu idanunsu bayan sun kwace musu duk wasu abubuwan su masu daraja.

“Sun tambayeni idan na yi aure sai na fada musu cewa ina da aure har da yara 2 amma ba gaskiya ba ne saboda irin mu ba mu aure,” a cewar ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here