Harin NDA: ‘Yan Bindigan Sun Nemi Kudin Fasar Manjo Dantong

 

‘Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci kudin fansa.

Yayinda suka kashe Sojoji biyu, ko mutum daya ba’a kashe cikinsu ba.

Wannan abu ya janyo suka iri-iri ga hukumar Sojoji.

Kaduna – Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jahar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami’in Soja sun kira gidan Soja.

Sojan da akayi awon gaba da shi sunansa, Manjo Dantong.

A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi.

Sun bukaci a basu kudi N200m idan har ana son Manjon ya dawo da ransa.

Wata majiyar FIJ ta bayyana cewa:

“Ko mutum daya sun kasa kashewa. Sun duba ko ina cikin daji amma basu gansu ba. Sun gudu kan baburansu.”

“Sun kira kuma sun bukaci kudin fansa N200m don sake Manjon. Wannan harin abin takaici ne. Sun shigo, sun mamaye mu kuma sun tafi.”

“Ko jirgi mai saukar angulun da aka tura yawo cikin daji bai gansu ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here