Hasashen Fada Mbaka ga Gwamnatin Buhari

 

Fada Mbaka ya yi hasashen cewa da yiwuwa a kwace mulki hannun Buhari idan bai tashi tsaye ba.

A cewarsa, wadanda ke kan ragamar mulki sun yi debi kudin Najeriya fiye da yadda ake tsammani.

Malamin ya ce Ubangiji na fushi da wadannan shugabannin kuma bala’i zai fado musu udan basu canza ba.

Ya yi gargadi cewa kada wannan yayi masa raddi kan wadannan hasashen da yayi ko kuma bala’in ya fara shi Wani malamin cocin Katolika, Rabaran Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa za’a kawo karshen mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Mbaka ya bayyana hakan ne a taron tarban sabuwar shekarar da ya saba yi kowace shekara a cocinsa ta Adoration Ministries dake jihar Enugu.

Ya ce wajibi ne shugaban kasan ya tashi tsaye ya ceci gwamnatinsa.

he Nation ta ruwaito Malamin da shawartan gwamna Buhari cewa ta samar da aikin yi kafin matasan Najeriya su tayar da tarzoman da kawo karshen mulkinsa.

Yace: “Ruhin ubangiji ya umurceni in gargadi gwamnatin yau cewa tayi a hankali ; ta canza salon mulkinta kuma ta kula da matasa ba tare da siyasantar da halin da suke ciki ba.”

“Gwamnati ta tashi tsaye ta samar da aikin yi da zai amfani matasan kasar saboda sun ji jiki sosai.”

“Kada ku siyasantar da halin da matasa ke ciki, idan ba haka, za su tashi tsaye ku su kawo karshen gwamnatin.”

“Idan gwamnatin ta ko yin hakan cikin gaggawa, matasa zasu yi fito-na-fito da gwamna, kuma idan akayi kokarin hanasu, karshen gwamnati ya zo.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here