Hatsarin Mota ya Hallaka Mutane 13 a Ghana

 

Mutum 13 sun rasa rayukansu sakamakon wata tahomu-gama da aka yi tsakanin motoci biyu a babban titin Konongo da ke yankin Ashanti a Ghana.

‘Yan sanda sun ce hadarin ya auku ne da misalin karfe 10:40 na yammacin jiya Lahadi.

A cewar DSP Paa Yeboah, hatarin ya yi sanadi rayukan maza 9 da mata 4, sannan akwai mutum 11 da suka jikkata.

Rahotanni sun ce motar fasinja dauke da mutum 26 da katuwar motar dakon kaya ne suka yi gware, kuma nan take mutum 13 suka mutu.

‘Yan sanda sun ce an kai gawwakin mutanen mutuware, yayinda aka dauki hotunansu iya tantancewa daga iyalai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here