Hatsarin Jiragen Sama: Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta Kafa Kwamitin Bincike

 

Rundunar sojojin saman Najeriya ta kafa kwamiti don binciken hadurran jiragen sama a Najeriya.

Rundunar ta bayyana damuwarta da yawaitar hadurran jirgin sojojin saman Najeriya a shekarar nan.

Kwamitin zai yi aiki ta fuskoki da dama don tabbatar da binciken kwa-kwaf kan lamarin hadurran.

Hukumar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hada wani kwamiti da zai binciki hadurran jirgin sama da ke ci gaba da faruwa.

Wannan na zuwa ne a cikin damuwar da ‘yan Najeriya suka nuna biyo bayan hadarin jirgin sama uku da ya faru a cikin watanni uku.

Hadarin ya haifar da asarar rayukan jami’an sojoji 18, ciki har da na makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban hafsan sojojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, Vanguard News ta ruwaito.

Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce kwamitin da Shugaban Hafsun Sojojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao ya kafa, ya kunshi ma’aikatan da suka yi ritaya.

Gabkwet ya bayyana cewa mambobin kwamitin za su gudanar da binciken lafiya na dukkan sassan NAF na aiki da injiniyoyi, ya kara da cewa CAS ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa kafin 18 ga watan Yuni, 2021.

A cewarsa, mataimakin kwamandan rundunar Operation HADIN KAI, Air Vice Marshal Abraham Adole ne zai jagoranci kwamitin, Daily Trust ta ruwaito.

“Kwamitin zai kuma yi aiki tare da rukunin masu aiki da ma’aikatan fasaha don ra’ayoyi, abubuwan lura da gudummawa kan matakan tsaro,” sanarwar ta karanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here