Kwale-Kwale ya Kife da Masu Maulidi 300 a Jihar Neja

 

Wata sanarwa da babban darekta hukumar agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ta ce akwai sama da fasinjoji 300 a cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar da yammacin ranar Talata.

Abdullahi Arah ya ce kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.

Kakakin hukumar ta agajin gaggawa ta jihar ya ƙara da cewa yanzu an ceto mutum fiye da 150 da ransu.

Sai dai wata sanarwa da shugaban ƙaramar hukumar ya fitar da gidan talbijin na Channels ya rawaito ta nuna cewa aƙalla gawarwaki 60 ne aka gano sannan kuma ana ci gaba da neman wasu daga cikin fasinjojin.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto ƙarƙashin jagorancin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da sauran mutane.

Ko a watan Satumban 2023, an samu kwatankwacin irin wannan, inda kwale-kwale ɗauke da fasinja 50 ya kife kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here